Bahrein

wasu yan adawa a kasar Baren da aka zartarwa hukumcin daurin rai da rai a gidan yari sun bukaci a sakesu

masu zanga zanga a birnin  Manama, Assabar 26 février 2011.
masu zanga zanga a birnin Manama, Assabar 26 février 2011. Reuters/Caren Firouz

Wasu shuwagabannin yan shi’a guda 2 yan adawar kasar Bahrain da aka zartarwa hukumcin daurin rai da rai, kan lafin hada baki dasu a cutar da gwamnati a yau talata a gaban kotun daukaka kara ta birnin Manama, sun bukaci kotun ta sallamesu kamar yadda lauyoyinsu suka bayyana.

Talla

Hasan Mashaimma shugaban kungiyar Haq da kuma wani shugaba a kungiyar Abdeljalil al-Singace da kafafunsa suka daina aiki, sun saidawa kotun irin azabar da aka yi masu bayan da aka kamasu a cikin zanga zangar kin jinin gwamnatin kasar ta barke a watan maris din bara.

A lokacin sauraren karar mutanen 2 daya bayan daya sun bukaci kotun ta sakesu, tare da bayyana kansu a matsayin yan kason fadin albarkacin baki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.