Syria-diflomasiya

Mahukumtan kasar Fransa su kyale jakadiyar Syriya a kasar ta ci gaba da zama a birnin Paris

Lamia Shakkour jakadiyar Syriya a Fransa
Lamia Shakkour jakadiyar Syriya a Fransa BFM.TV

Bayan da ta kasance daga cikin jerin jami’an kasar Syriya da aka kora sakamakon kisan rashin imanin garin Hula, a yau laraba mahukumtan kasar Fransa sun baiwa jakadiyar kasar Syriya a kasar uwargida Lamia Shakkour damar ci gaba da zama a birnin Paris, sakamakon kasancewarta mamba a hukumar raya al’adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO wace babban ofishinta ke birnin Paris.

Talla

A lokacin da aka tambaye shi kan tafiyar jakadiya Shakkour daga Faransa, kakakin ma’aikatar ministan harakokin wajen kasar Fransa Bernad Valero, ya shaida wa manema labarai cewa, uwargida Shakkour na daya daga cikin jami’an da ba a son  gani a matsayinta na jakadiyar kasar Syriya, amma kuma a dai gefen ita ce wakiliyar Syriya a hukumar raya al’adu ta Majalisar dinkin duniya, dan haka kasar Fransa na mutunta yarjejeniyar Majalisar dinkin duniya ba zata koreta ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.