Masar

Za a sake gurfanar da 'ya 'yan tsohon shugaban kasar Masar Husnil Mubarak su 2 a gaban kotu

Gamal Moubarak daya daga cikin ya yan tsohon shugaban kasar Masar Husnil Mubarak
Gamal Moubarak daya daga cikin ya yan tsohon shugaban kasar Masar Husnil Mubarak AFP

Ya yan tsohon shugaban kasar Masar Husnil Mubarak, da aka tuni aka yiwa shara’a kan laifuffuka daban daban na karkata dukiyar kasa, na kan shirin gurfana a gaban wata sabuwar shara’a ta cin hanci, kamar yadda tashar talabijin din gwamnatin kasar ta sanar a yau laraba.

Talla

Gamal da Alaa ya’yan hambararen shugaba Mubarak da ake ci gaba da yi wa daurin talala a birnin kairo, yanzu haka dai za’a sake gurfanar da wadannan yara ne tare da wasu mutane 7 kan laifin cin hanci da rashawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.