Iran

Ahmadenijad yace kera makamashin Uranium hakkin Iran ne

Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad a lokacin da yake zantawa da kafar Telebijin ta France 24.
Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad a lokacin da yake zantawa da kafar Telebijin ta France 24. France 24

Shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad yace samar da makamashin Uranium da suke yi hakkin kasar Iran ne, ba suna kokarin kera makamin Nukiliya ne ba bayan Amurka ta yi kiran zama teburin tattaunawa da Tehran.

Talla

Shugaba Mahmud Ahmadinejad ya fadawa tashar Telebijin ta France 24 cewa karkashin Dokokin duniya, aikin samar da Nukiliya da kasarsa ke yi hakkin kasar ne.

Shugaban ya karyata bayanan da ke cewa Iran tana hada munanan makamai ne.

Ahmadinejad yace Hukumar Sa Ido kan aikin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, ya dace ta bai wa kasar Iran izinin samar da sinadarin Uranium akalla kashi 20%.

Yace saboda rasa sinadarin ne yasa Kasar ta yi gaban kanta, wajen aikin da take yi, kuma abin bukata shi ne a fito fili a shai da masu makasudin hana su aikin.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da kudurori 6 da ke bukatar kasar Iran ta dai na aikin samar da Uranium bayan kakuba ma kasar jerin takunkumi har guda hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.