Palasdinu-MDD

Palasdinawa sun nemi a yi bincike kan mutuwar Arafat

Mai shiga tsakanin na kungiyar Palasdinu Saeb Erakat.
Mai shiga tsakanin na kungiyar Palasdinu Saeb Erakat. AFP/Abbas Momani

Kungiyar Palasdinawa, ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da bincike kan mutuwar Yaseer Arafat, bayan wani bincike da wata cibiyar tayi, ya nuna cewar guba ne, ya kashe shi.Bukatar kungiyar Palasdinwa, ta hannun mai shiga tsakanin Saeb Erakat, da kuma matar Tsohon shugaban Palasdinawan, Suha, ya biyo bayan wani bincike da Cibiyar binciken Switzerland tayi, wanda ya gano wani sinadarin polonium, a jikin kayan sa, lokacin da ya rasu a Paris, a matsayin abinda ya kashe shi.Daraktan Cibiyar da ya gudanar da binciken, Francois Bochud, ya tabbatar da gano sinadarin, wanda yace yana da hadari sosai ga lafiyar Bil Adama.Daraktan yace, abin yi kawai shine tono gawar Arafat, domin gudanar da bincike akai cikin gaggawa, domin duk wani jinkiri na iya sanya shaidar ta gushe.Wannan bincike ya dada tado da zargin da ake na cewa, an kashe tsohon shugaban na Palasdinawa ne, saboda matsayin sa na ganin al’ummar sa ta samu kasa na kanta.Kuma kisan nasa na zuwa ne, shekaru hudu da fara zanga zanga, bayan an kwashe shekaru da dama ana tattaunawa tsakanin Israila da Palasdinawa ba tare da cimma wani abin kirki ba.Shi dai Arafat ya jagoranci Palasdinawa daga shekarar 1960, inda ya sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a shekarar 1993, dan kafa hukumar Palasdinu a Gaza da Gabar Yamma da kogin Kordan.Erakata yace suna bukatar kwamitin bincike irin wadanda Majalisar Dinkin Duniay ta sa, ya binciki kisan Rafiq Hariri, Tsohon Prime Ministan Lebanon.