'Yan Pakistan na zanga zangar kin anicewa da NATO
Wallafawa ranar:
Dubban Yan kasar Pakistan ne, daga sassa dabam dabam, suka yi gangami a birnin Islambad, don nuna bacin ransu da yadda kasar ta bar kungiyar tsaro ta NATO ta dinga wucewa da kayan sojin ta zuwa Afghanistan.Zanga zangar itace mafi girma, tun bayan sake bude hanyar, sakamakon rufewar da aka yi, lokacin da Amurka ta kashe sojin kasar 24, a wani harin da kai ta sama.