Isra'ila

Obama ya yi tir da saka siyasa cikin matsayar Amurka kan Isra’ila

President Barack Obama at the National Association of Latino Elected and Appointed Officials, Florida, 22 June, 2012
President Barack Obama at the National Association of Latino Elected and Appointed Officials, Florida, 22 June, 2012 Reuters/Kevin Lamarque

Shugaban Kasar Amurka Barack Obama ya ce zakewar da kasar shi ke yi wajen goyon bayan Isra’ila ba wani abu da za a yi ta muhawarar siyasa kan shi ba ne. Obama wanda ke jawabi lokacin da ya isa Jihar Florida, a ci gaba da yakin neman zaben da yake yi, ya kuma yi Allah wadai da harin bom da aka kai wa motar bas din nan, da ke shake da yahudawa, ‘yan yawon bude ido a kasar Bulgariya.  

Talla

Lamarin ya yi sanadiyya mutuwar yahudawan 6, kuma tuni Isra’ila ta dora alhakin harin kan Iran.
 

A cewar Obama kasar Amurka za ta cigaba da karfafa dangantakarta da kasar Isra’ila duk da cewa ana sukan yin hakan.
 

Ya kara da cewa wannan lokaci shi dai dai da ya kamata kasar Amurka ta kare kasar Isra’ila kuma hakan bai kamata ya jawo muhawarar siyasa ba.

Jihar ta Florida na daya daga cikin jihohi a kasar Amurka da ke da yawan Yahudawa inda wani bincike da Jami’ar Connectitut ya nuna cewa kashi goman Yahudawan Amurka na zaune a Jihar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.