Afghanistan

Taliban ta yi kiran kawo karshen yaki a Afghanistan

Shugabannin kungiyar Taliban sun yi kiran kawo karshen Yaki a kasar Afghanistan da aka kwashe tsawon shekaru 10 ana yi. Kungiyar ta nemi sasantawa tare da neman bukatar sakin mayakanta da ake tsare da su.

Sansanin Mayakan Taliban a Afghanistan
Sansanin Mayakan Taliban a Afghanistan ( Photo : AFP )
Talla

A wata sanarwa da Mulla Agha Jan Motasim ya aikawa kamfanin Dillacin Labaran Faransa AFP, Kungiyar Taliban ta nemi tsagaita wuta domin zaunawa a teburin sasantawa.

Motasim wanda shi ne Ministan Kudi a zamanin Mulkin Taliban tsakanin shekarar 1996 zuwa 2001, ya yi kiran janye Takunkumin hana yawo da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa wasu manyan Mambobinsu.

Sai dai ya nemi Majalisar Dinkin Duniya da Amurka su soke sunan Taliban daga cikin sunayen kungiyoyin ‘Yan ta’adda da kuma sakin ‘yayan kungiyar da ake tsare da su a Guantanamo Bay.

"Mun yi imanin kasashen Duniya za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa” inji Motasim.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI