Indiya

‘Yan adawa a Majalisar Indiya sun nemi Firaminista yin murabus

‘Yan adawa a zauren majalisar kasar Indiya sun dauki matakin haramta zaman Majalisa har sai Firaministan kasar ya yi murabus akan badakalar kudaden albarkatun kasa na Kwal bayan fitar da Wani Rahoto wanda yace gwamnatin kasar ta yi hasarar Biliyoyin daloli.

Firaministan India, Manmohan Singh
Firaministan India, Manmohan Singh REUTERS/Andrew Biraj/Files
Talla

Firaminista Manmohan Singh shi ne Ministan kula da Kwal kuma yana cikin wadanda ake zargin sun yi rub da ciki da kudaden Gwamnati.

Madugun adawa a zauren Majalisar Indiya, Arun Jaitley yace Jam’iyyarsu ta BJP zata yi kokarin dakile zaman Majalisa har sai Manmohan Singh ya amsa zargin da ake ma shi tare da yin murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI