India

Kotun Indiya ta yanke wa dan harin Mumbai hukuncin Kisa

A yau Laraba, kotun kolin kasar India ta tabbatar da hukuncin kisa, ga wani mutum mai suna Mohammed Kasab da ya rayu, cikin ‘Yan bindigan da suka kai hari a birnin Mumbai, a shekarar 2008.Mohammed Kasab yana daya daga cikin mutane 10 da suka kai harin da suka shafe kwanaki uku, da ya yi sanadiyyar rasa ran mutane 166. Amma kuma ya daukaka karar hukuncin da aka yanke masa.

Mohammed Ajmal Amir Kasab a lokacin da ya ke hannun 'Yan Sandan India
Mohammed Ajmal Amir Kasab a lokacin da ya ke hannun 'Yan Sandan India Reuters
Talla

A shekarar 2010 aka same shi da laifin kaddamar da yaki kan kasar India da laifin kisan kai da aikata ta’addanci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI