India

An tsinci wata jakar wasikokin diplomasiyar India bayan shekaru 46

An tsinci wata jaka dauke da wasikar diplomasiyar da kasar India ta aika tun a shekarar 1966 a tsaunin Mt. Blanc da ke nahiyar Turai. Wasikar an tsince ta ne kusa da inda wani jirgin kasar India ya fadi a shekarar ta 1966. 

Wani jirgin India da ya taba faduwa
Wani jirgin India da ya taba faduwa REUTERS/Stringer
Talla

Wani ma’aikacin ceto, da ake kira, Arnoud Christmann, ya tsinci jakar wacce ke dauke da tambarin da aka rubuta “wasikar diplomasiya” da kuma “Ma’aikatar harkokin waje”.

A cewar Christmann, wasu ‘Yan yawan bude ido ne su ka gaya musu cewa sun hango wani abu mai kyalli a kasan tsaunukan na Mt. Blanc, inda ya gayyaci makwabtansa da su je su ga ko menene.

“Mun tsinci burbushin jirgi, da takalmi da wasu wayoyi”, inji Christmann, a hirarsa da Kamfanin Dillancin labaran Faransa.

Ya kara da cewa, a da sun sa ran za su tsinci zinare amma sai su ka tsinci wasiku a jike da wata jaridar kasar India.

An dai tabbatar cewa, wani jirgin kamfanin Kangchenjunga, Boeing 707, wanda ya taso daga Mumbai zuwa birnin New York a kasar Amurka, ya fadi a kudu maso gabashin tsaunukan nahiyar Turai.

Jirgin dai ya fadi a ranar 24 ga watan Janairun shekarar 1966, a lokacin da jirgin ke kokarin yada zango a birnin Geneva da ke kasar Switzerland.

Bincike ya nuna cewa, duk mutanen su 117 da ke cikin jirgin sun halaka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI