Wani ya kashe kansa a Sin, ya raunata mutane shida
Saboda rashin gamsuwa da rashin adalcin da ya yi zargin ana nunawa, wani mutumin karkara a gabashin kasar Sin ya ta da bam a wani ginin karamar hukuma, inda ya kashe kansa ya kuma raunata mutane shida.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mutumin wanda ake kira, Qu Huaqiang, rahotanni sun nuna cewa ya shigar da wata kara ne a rubuce, koda yake ba a fadi menene kokensa ba.
Haka kuma ba a tabbatar ko wadanda su ka ji raunukan ma’aikatan karamar hukumar ne ba.
Wani jami’i a garin Tengjia, ya tabbatarwa da Kamfanin Dillancin labaran AFP,da aukuwar lamarin, sai dai ya musanta cewa, Huaqiang ya shigar da wata kara a rubuce.
Tuni dai labarin ya bazu a yanar gizo inda ‘Yan kasar ke ta tofa albarkacin bakinsu kan lamarin.
Tattalin arzikin kasar ta Sin, duk da cewa ya bunkasa a cikin shekaru 30 da su ka wuce, ya janyo babban gibi tsakanin masu hanu da shuni da talakawan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu