India

India da Sin za su dawo da shirin atisayen sojoji

Wasu sojojin kasar India akan iyakar kasar
Wasu sojojin kasar India akan iyakar kasar Reuters

Kasashen India da Sin za su dawo da atisayen sojojin kasashen biyu da su ka saba a da.A da kasashen biyu kan gudanar da atisayen tare, amma kara gurbacewar kawance tsakanin kasashen biyu a shekarar 2008, ya sa su ka dena gudanar da atisayen. 

Talla

Ministan tsaron kasar India, A.K Antony ya bayyana hakan bayan wata ganawa da su ka yi da takwaransa na kasar Sin, Janar Liang Guanglie a birnin New Delhi.

India da Sin na daga cikin kasashe biyu a nahiyar ta Asiya da ke tashen ta fannin tattalin arziki da kuma cigaba.

Matsalar kan iyaka tsakanin kasashen shi ke kawo cikas tsakanin kasashen biyu inda aka kasa samun mafita tun daga shekarar 1962.

A lokacin ya kai ga kasashen biyu sun tafka yaki na dan wani lokaci inda akan kan iyakar da ke Arewacin kasar India

Wani mai Magana da yawun kasar India, ya kara tabbatar da cewa ministocin biyu sun kuma tattauna akan yadda za a magance matsalar ‘Yan fashin teku Gulf na Aden da ke wajen kasar Somalia.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.