India
Mutane 10 sun mutu a kamfanin hada kayan wuta a India
Wani abu da ya fashe a kamfanin hada kayan wuta da ke kudancin kasar India ya kashe akalla mutane 10, a cewar wani rahoto.
Wallafawa ranar:
Talla
Wani rahoton gidan telebijin kasar ya nuna wani turnikewan hayaki a saman kamfanin, wanda shi ne cibiyar hada kayayyakin wuta a kasar at India.
Kafofin yada labarai sun nuna cewa mutane 10 ne su ka mutu, sai dai ‘Yan sanda a kasar ba su fadi adadin mutanen da su ka mutu ba.
Sai dai wata sanarwa da wani jami’in tsaro a kasar ya fitar ya nuna cewa an kwashe gawawwaki 20, sai dai bai fadi duka adadin mutanen da su ka mutu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu