Mataimakin shugaban babban sojin Amurka ya gana da ministan tsaron Isra’ila
Wallafawa ranar:
Mataimakin shugaban babban sojin kasar Amurka, Admiral James Winnefeld, ya gana da Ministan tsaron kasar Isra’ila, Ehud Barak, a dai dai lokacin da batun sarrafa sinadarin Nukiliya da kasar Iran ke yi, ya yi tsamari.
Wata takardar sanarwa da ma’aikatar kasar ta Isra’ila ta fitar ta nuna cewa, Winnefeld, ya gana da Ehud ne a ofishinsa da ke Tel Aviv.
Sai dai sanarwar ba ta ba da cikakken bayanin abin day a gudana a ganawar ba.
Winnefeld ya kai ziyar ce, bayan ya samu gayyatar takwaran nasa na kasar Isra’ila, a cewar, mataimakin, babbaan sojin kasar ta Isra’ila, Janar Yair Naveh.
Rahotanni sun nuna cewa ba a san lokacin da Winnefeld ya isa kasar ta Isra’ila ba amma a ranar Alhamis zai koma.
An samu takaddama a ‘yan kwanakin nan a tsakanin kasashen biyu, ta dalilin ikrarin da ake yi da ke nuna cewa kasar ta Isra’ila, na kokarin kai hari kasar Iran ba tare da fadar White House ta Amurka ta ba da izinin yin hakan ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu