Kotun Vietnam ta yankewa wani Dan jarida hukuncin shekaru hudu a gidan yari
Wallafawa ranar:
Wata kotu a kasar Vietnam ta yankewa wani Dan jarida mai yaki da cin hanci da rashawa a kasar, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru hudu. Hoang Khuong, dan shekaru 39, wanda kuma ya ke aiki da jaridar Tuoi Tre, an same shi ne da laifin ba da cinhanci ga wani Dan sanda mai kula da ababan hawa.
Kudin, a cewar Kamfanin Dillancin labaran AFP, ya kai kudi dalar Amurka, 715 don Dan sandan ya taimaka wajen sako wani babur da aka kama.
Dan sandan, wanda shi ma ya karbi cinhancin an yanke mai hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar, a wata sha’ria da aka musu tare da Khuong.
Wata kungiyar ‘Yan jarida wacce bata da sanke ta kasar Faransa, a da ta ce, Khuong ya ba da cinhancin ne a wani bincike da ya ke gudanarwa.
A shekarar 2008, an kulle wani Dan jarida na tsawon shekaru biyu bayan ya yi wani rahoto akan wata badakala da aka yi a ma’aikatar sufurin kasar ta Vietnam, wacce kara ce da ta ja hankalin mutane da dama a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu