Wasu harin bama bamai sun kashe mutane takwas a Iraq
Wallafawa ranar:
Wasu hare haren bam bamai da aka kai kan ‘Yan shi’a a Khezal al – Tamimi Husseiniyahs da ke Arewacin kasar Iraq, ya kashe mutane takwas.Shugaban fannin kiwon lafiya a Kirkuk, Sadiq Omar Rasul, ya tabbatarwa, Kamfanin Dillancin labaran Faransa cewa mutane takwas sun mutu a yayin da wasu 33 su ka jikkata.
Wani wakilin AFP, wanda ya ga gawawwakin ya ce akwai yara guda biyu a ciki a yayin da motoci da dama sun kone.
Haka kuma wani da aka yi abun akan idonsa, Hassan Hussein, ya kara da cewa, suna daura laifin akan Firaministan kasar inda ya kara da cewa, suna so ya karesu daga hare haren.
Khezal al- Tamimi dai wuri ne da ofishin babban malamin nan na ‘Yan Shi’, Moqtada al Sadr yake.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu