Isra'ila

Isra’ila ta ce ba za ta jira sauran kasashen duniya ba in za ta dauki mataki kan Iran

Firaministan kasar Isra’ila. Benjamin Netanyahu ya ce, kasar Isra’ila ba za ta jira sauran kasashen duniya ba idan har za ta dauki mataki akan kasar Iran. “kasashen duniya na cewa mu tsaya, wai akwai lokaci, ni kuma na ce musu, mu tsaya mu jira me?, mu tsaya mu jira sai yaushe,” inji Netanyahu. 

Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu Reuters
Talla

Netanyahu ya fadi hakan ne a wani zama da su ka yi da takwaransa na kasar Bulgaria, Boyko Borisov.

Ya kuma kara da cewa hanyoyin da aka bi na diflomasiya da saka takunkumi duk basu yi amfani ba, inda ya kara jaddada cewa akwai bukatar a takawa kasar ta Iran burki akan Uraniyom da ta ke sarrafawa domin hada makamshin Nukiliya.

A ‘yan makwannin da su ka gabata, shugaban na Isra’ila, ya nuna bukatar kasashen duniya da su takawa kasar ta Iran burki domin a gujewa fadawa cikin yaki.

Kasar Isra’ila wacce ita kadai ke da makamin Nukiliya a gabas ta tsakiya na ikrarin cewa barin Iran ta hada makamin Nukiliya zai zama barazana ga kasar ta Isra’ila, inda ta nuna akwai yiwuwar kai wa Iran hari idan har ana so ta gujewa yin hakan.

Kasar Amurka da kasashen yammacin duniya sun yadda da cewa Iran na sarrafa Uraniyom ne domin hada makamshin Nukiliya, zargin da kasar Iran ta dade tana musanta.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI