Pakistan

Gobara ta yi sanadiyar mutuwar mutane 30 a Pakistan

Gobarar wuta da aka samu a wasu masana’antu biyu a kasar Pakistan, sun yi sanadiyar hallaka ma’aikata 30, yayin da wasu 34 suka samu raunuka. An samu gobarar ne a Lahore, da ta ritsa da ma’aikatan kamfanin samar da takalma. Wani jami’in agajin gaggawa, Karamat Ali, yace sun kai gawawwaki 21 zuwa asibiti, tare da wadanda suka samu raunuka 14.

Taswirar Yankin Lahore a kasar Pakistan
Taswirar Yankin Lahore a kasar Pakistan RFI/Devrim Alpoge