Sin za ta bude reshen bankinta a Luxembourg
Kasar Sin za ta bude reshen bankita na kere-kere a Luxembourg, a cewar wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar. Sanarwar bude reshen bankin ta biyo bayan wata tattaunawa da aka yi tskanin shugaban bankin na Sin, wato, Wang Hongzhang, da kuma Firaministan Luxembourg, Jean- Claude Junker da kuma Ministan kudi, Luc Frieden.
Wallafawa ranar:
A cewar sanarwar, za a bude reshen bankin ne nan ba da dadewa ba, saboda daidaituwar tattalin arzikin kasar.
A yanzu haka dai akwai, bankunan kasar Sin guda biyu a Luxembourg, wadanda su ka hada da bankin ma’aikatu da kuma bankin kasuwanci na Sin, wato (ICBC).
Wadannan bankuna sun bude rassansu ne na nahiyar Turai ne a shekarar 2011.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu