Afghanistan

Mutane 50 sun mutu a wata taho mu gama a Afghanistan

Wani harin Bom da aka taba kai wa a yankin Ghazni
Wani harin Bom da aka taba kai wa a yankin Ghazni Reuters

Akalla mutane 50 suka mutu bayan wata taho mugama da Motar Fasinja ta yi da Tankar mai, inda wasu da dama suka samu rauni da suka hada da mata da kananan yara. Al’amarin ya auku ne a yankin Ghazni gundumar Ab Band saman babban titin Kabul zuwa Kandahar hanya mafi muni a Afghanistan.