Mutane 1000 sun fito sabuwar zanga zanga a Afghanistan
Akalla mutane 1,000 suka shiga wata sabuwar zanga zanga yau a birnin Kabul dake kasar Afghanistan, dan cigaba da adawa da fim din da ya ci zarafin addinin Islama. Rahotanni sun ce, akasarin masu zanga zangar daliban jami’a ne, wadanda suka yi ta kalaman batanci ga Amurka.
Wallafawa ranar:
Masu zanga zangan, sun tare manyan hanyoyi a yayin da su ke nuna bacin ransu akan fim din.
Akalla mutane 30 su ka mutu akan fim din wanda aka wa lakabi da “Innocence of Muslims” wanda ya muzanta Annabi Muhammad S.A.W., tun da aka fara nuna kin jinin kasar Amurka, wacce ita ce kasar wanda ya hada fim ya ke.
Kasar Afgahnistan na da tarihin gudanar da zanga zanga wanda kan jirkice ya koma hare hare, musamman idan abin ya shafi muzunta addinin Islama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu