India

Za a shiga yajin aikin gama gari a India

Firaministan kasar India, Manmohan Singh
Firaministan kasar India, Manmohan Singh www.theunrealtimes.com

Miliyoyin ‘Yan kasuwa da Yan dako ne ake saran yau zasu bi sahun ma’aikatan India, dan shiga yajin aikin gama gari, dan adawa da barin Yan kasuwan kasashen waje su mamaye kasar. Jam’iyun adawa da kungiyoyin ma’aikata suka kira yajin aikin, bayan Prime Minister Manmohan Singh ya sanar da wasu sabbin matakan da yake ganin zasu bunkasa tattalin arzikin kasar. 

Talla

Kungiyar ma’aikatan kasar tace, tana saran mutane miliyan 50 su shiga zanga zangar da zasu yi yau.

Da yawa daga cikin ‘Yan kasuwa na ganin cewa shigowar manyan shagunan kasuwanci zai kawo rashin ayyuka a kasar ta India.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.