Fararen hula 30 sun mutu a rikicin Syria
Wallafawa ranar:
Akalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu a jiya Alhamis bayan fashewar wani abu a wani gidan mai sakamakon harin da dakarun kasar Syria suka kai ta sama a yankin Arewacin kasar, kamar yadda kungiyoyin fararen hula suka sanar.
Mutane da dama ne su ka kuma jikkata a wajen da fashewar ta faru da ke Arewacin kauyen Ain Issa.
A daya gefen kuma ‘Yan tawayen kasar, sun bayyana kakkabo wani jirgin helicoptan sojan Syria a kusa da Damas, inda yan adawa suka bayyana cewa, mutane sun fice daga unguwarninsu sakamakon kazamin fadan da ake tabkawa.
Sai dai gidan talbijin na Kasar ya rawaito cewa, jirgin ya fadi ne bayan ya yi karo da wani jirgin farar hula.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu