Faransa ta tabbatar da mutuwar ‘Yan kasarta hudu a hadarin rugujewar tsaunukan kankara
Ofishin harkokin wajen kasar Faransa, ya tabbatar da mutuwar mutane hudu, ‘Yan kasar ta Faransa wadanda su ka rasa rayukansu a hadarin rugujewar tsaunukan kankara da ya auku jiya a kasar Nepal.
Wallafawa ranar:
“A irin binciken da mu kayi na farko, ‘Yan kasar Faransa hudu sun rasu a wannan hadari” inji Minista mai kula da Faransawa a kasashen waje, Helene Conway – Mouret, a wata sanarwa da aka fitar.
Masu ayyukan ceto su na ta kokarin nemo biyu daga cikin Faransawa da wani Dan kasar Canada wadanada suna cikin jama’ar da su ka bace a hadarin.
Hukumomi a kasar Nepal a da sun bayyana cewa wadanda hadarin ya rutsa da su sun hada Faransawa hudu, Dan kasar ta Nepal daya, da Dan kasar Spain da wani Bajamush da kuma Dan kasar Italiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu