Japan za ta aika Jami’in diplomasiya zuwa Sin
Kasar Japan tace zata tura babban jami’in diplomasiyar ta zuwa kasar China dan kawo karshen takaddamar da ta shiga tsakanin kasashen biyu, wanda ya haifar da munanan zanga zanga. Mataimakin Ministan harkokin wajen kasar, Chikao Kawai, zai gana da takwaran shi a ziyarar da zai kai, kan halin da ake ciki, da kuma matakan da ya kamata a dauka dan gyara.
Wallafawa ranar:
Matakin na zuwa kwana guda bayan China ta dakatar da wani biki na cika shekaru 40 na danganataka tsakanin kasashen biyu.
Kasashen biyu dai sun dade suna kai ruwa rana akan wasu tsibirai da dukkaninsu ke ikrarin nasu, a yayin da kasar Taiwan ita ke ikrarin cewa nata.
Al’amuran sun kara tabarbarewa ne a lokacin da gwamnatin Japan ta saye wuraren daga hannayen wadanda ke mallakar tsibiran.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu