Japan

Japan ta gargardi Sin kan barazanar da ta ke nunawa akan rikicin tsibiru

Firaministan Japan, Yoshihiko Noda
Firaministan Japan, Yoshihiko Noda REUTERS/Issei Kato

Firaministan kasar Japan, Yoshiko Noda, ya gargadi kasar Sin, wato China, cewar ba zasu lamince da duk wata barazana daga China ba, kan rikicin tsibirun dake tsakaninsu, yayin da ya bayyana bacin ransa kan yadda ake kai hari kan muradun su. Yayin da yake bayani ga manema labarai a New York, ya ce China ta kasa fahimtar halin da ake ciki, domin tarihi ya nuna cewar, wadanan tsibiran mallakar Japan ne.  

Talla

Noda yace ta hanyar tattaunawa ne kawai za’a iya magance matsalar amma ba barazana ko bude ido ba.

A jiya ne dai Kamfanin kera motocin Toyota da Nissan mallakar kasashen Japan, suka rage yawan motocin da su ke kerawa a China, saboda faduwar kasuwa, sakamakon takkadamar.

Mai Magana da yawun Toyota, yace sun rage yawan motocin da suke kerawa yanzu haka, yayin da Nissan tace zasu dakatar da kera motocin har zuwa bayan watan October mai zuwa.

“Abokanan huldanmu na rage ayyukansu suna masu la’akkri da yadda ake neman motocin.” Inji mai Magana da yawun Kamfanin Toyota.

Ya kara da cewa, basu fara hada wasu motocin ba har sai bayan watan Oktoba, bayan sunyi la’akkari da yadda kasuwa za ta kasance.

Kasashen Japan dai na takaddama tsakaninsu akan wasu tsibirai da dukkaninsu ke ikrarin cewa mallakarsu ne,,abin day a jawo zanga zangar kin jinin Japan bayan ta saye tsibiran daga hannayen masu shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI