Isra'ila

Isra’ila ta ce harin roka daga Syria ba dan ya sauka a kasarta ba ne

Wani Ministan kasar Isra’ila ya ce rokar da aka harbo daga Syria wanda ya fada a yankin Golan Heights kuskure ne, inda ya kara da cewa harin ba ana nufin ya sauka a Isra’ila bane. “Rokar ta fado cikin kasarmu ne ta dalilin gumurzun da ake yi a Syria, kuma mu bamu da niyyar mu saka kanmu a cikin wannan batu,” inji Ministan Raya Yankunar Isra’ila, Silvon Shalom. 

Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu Reuters/Lior Mizrahi/Pool
Talla

A jiya ne dai wata roka da aka harbo daga Syria ta fada yankin Golan Heights inda ta fashe amma ba tare da ta raunata ko mutum daya ba.

A shekarar 1967 ne kasar ta Isra’ila ta karbe yankin Golan Heights daga kasar Syria bayan wani fada da aka kwashe kwanaki shida ana yi, inda daga baya ta hade shi da kasarta a shekarar 1981.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI