Pakistan

Amurka da Pakistan sun janye taron Hafsohin sojinsu saboda zanga zanga

Wata zanga zangar nuna kyamar Amurka da aka gudanar a Pakistan
Wata zanga zangar nuna kyamar Amurka da aka gudanar a Pakistan REUTERS/Khuram Parvez

Kasar Amurka da Pakistan sun janye wata tattaunawa da Manyan Hafsoshin sojin kasashen biyu za su yi saboda zanga zanga da ake fama da ita da ke nuna kyamar Amurka. Wani Babban Hafsan sojin kasar Amurka, Janar Martin Dempsey, ya sanar da hakan, a wani taron manema labarai, inda ya kara da cewa, tattaunawar wacce aka yi niyyar gudanar da ita cikin sirri a Pakistan an dage ta. 

Talla

A taron tattaunawar, a da na sa ran, Dempsey zai gana da takwaransa na Pakistan, Janar Ashfaq Kayani, amma duk sun yi shawarar cewa a jenye tattaunawar.

Kasar Pakistan da wasu kasashen larabawa har ma da Turai, na fama da zanga zanga a ‘yan kwanakinnan, tun bayan fitar wani Fim da ya muzantawa addinin Islama, wanda kuma a kasar Amurka aka shiryasa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI