Iraqi

Mutane 13 sun mutu a harin Gidan- yarin Iraqi

Wani wuri da Dan Kunar-Bakin wake ya kai hari a Iraqi
Wani wuri da Dan Kunar-Bakin wake ya kai hari a Iraqi Reuters

A kalla 'Yan sanda 13 ne aka kashe a cikin wata musayar wuta da suka yi da wasu ‘Yan tsageru da suka kai wa Gidan Yari, a garin Tikrit dake Yankin Arewacin kasar Iraqi hari. Majiyar Mahukunta ta bayyana cewa, wani Dan Bunar Bakin - wake ne, cikin wata mota ya fara tarwatsa kansa da kuma kofar shiga gidan yarin, kafin daga bisani, sauran ‘Yan tsageran dake dauke da makamai suka kutsa kai a ciki. 

Talla

Harin da aka kai a kan gidan yarin dai ya samu madauka nauyi, inda kungiyar nan mai fafatukar kafa gwamnatin musulunci a kasar Iraqi ta ISI, wanda reshe ne kungiyar Alqa’ida tace ita keda alhakin yin haka, bayan da tun kafin wannan lokaci ta bayyana aniyarta na kubutar da daukacin ‘ya’yanta da ake tsare dasu a gidajen yarin kasar

Wata majiya daga cikin ‘Yan sanda da suka fafata da yan tsageran, ta bayyana cewa ‘Yan sanda 15 ne suka kwanta dama tare da Fursunoni guda 7 a yayinda wasu 34 suka jikkata.

Mataimakin gwamnan yankin, Ahmad Abdul jabbar, ya bayyana cewa fursunoni 83 sun yi amfani da damar da suka samu a lokacin bata- kashin, inda suma suka tsere.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI