Syria

An nemi kasashen Larabawa da Latin Amurka su hada kai don magance rikicin Syria

Wani wuri da aka kai hari a rikicin Syria
Wani wuri da aka kai hari a rikicin Syria Reuters

Sakatare Janar na kungiyar kasahsen Larabawa, Nabil al Arabi, ya bukaci kasashen Gabas ta Tsakiya da Latin Amurka, da su hada kai dan magance rikicin kasar Syria.

Talla

Yayin da yake jawabi wajen taron kasashen da suka fito wadannan Yankuna, Al Arabi yace duk matakan da ake dauka wajen ganin an magance rikicin Syria sun kasa cimma biyan bukata.

Sakataren ya kuma bukaci goyan baya kafa kasar Palasdinu a jawabin nasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI