Iran

Baza mu janye da shirinmu na Nukiliya ba, inji Ahmadinejad.

Shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmadinejad
Shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmadinejad

Shugaban Kasar Iran, Mahmud Ahmainejad, yace ba zasu janye kan shirin su na samun nukiliya ba, duk da matsalolin da kasahsen duniya suka haifar kasar, da suka hada da faduwar darajar kudin kasar. Yayin da yake ganawa da manema labarai, shugaban yace su ba mutane ne masu ja da baya akan shirin su na Nukiliya bane, saboda haka idan wani yana tunanin zai yiwa kasar Iran barazana gara ya sauya matsayin sa. 

Talla

A wani bagaren kuma, rahotanni na nuna cewa ana samun arangama tsakanin ‘Yan sanda da ‘Yan kasar ta Iran, saboda faduwar darajar kudin kasar na Rial data faru.

A satin nan dai darajar kudin na Iran ya rasa fiye da rabi darajarsa.
Rahotanni sun ce an hango tashin hayaki a wani yanki na babban birnin Tehran.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI