korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta yi barazanar kai hari Koriya ta Kudu

Shugaban kasar Korea ta Arewa, Kim Jong Un
Shugaban kasar Korea ta Arewa, Kim Jong Un

A yau juma’a rundunar sojan kasar Korea ta Arewa ta lashi takobin far wa makwabciyar ta Korea ta kudu, in har hukumomin Birnin Seoul basu dakatar da wani tsarin da suke shirin fara yi ba.

Talla

Wannan barazanar ta z one, kwana daya bayan shugaban kasar Korea ta Kudu, Lee Myung-Bak, ya kai wata ziyara bazata a wani tsibiri kusa da kan iyakan ruwa da kasashe ke takaddama akai.
 

Tuni dai kasar ta Korea ta Kudu, ta mayar da martanin cewa a shirye take ita ma ta kai

hari kan kasar ta Koriya ta Arewa muddin ta kai mata hari.
“Idan har suka kai mana hari, muma zamu mayar masu da martani,” inji Ministan tsaron kasar Korea ta Kudu, Kim Kwan –Jin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI