Jordan

Gwamnatin Jordan ta cafke mutane 11 da suka yi yunkurin kai hare hare

Sarki Abdullah na Jordan
Sarki Abdullah na Jordan AFP Photo/Jewel Samad

Gwamnatin Kasar Jordan tace ta gano wani yunkuri na kai hari kan ofishoshin Jakadaun kasashen Yammacin duniya da kuma shagunan kasuwanci da wasu da ake zargin ‘Yan kungiyar Al Qaeda suka kitsa, inda ta kama mutane 11. Kakakin gwamnatin kasar, Samih Maayta yace an kama wadanda ake zargin, bayan sun shiga kasar da makamai daga Syria, kuma yanzu haka suna tsare.