Sin

Har yanzu tsugune ba ta kare wa Bo Xilai ba a China

Primiyan kasar Sin, Wen Jiabao.
Primiyan kasar Sin, Wen Jiabao. Reuters

An fara bincike kan dan siyan nan na kasar Sin, mai suna Bo Xilai, bayan da aka kore shi daga majalisar dokokin kasar, da kwabe mishi rigar kariya. Wannan sanarwar na zuwa ne a daidai loacin da ake ci gaba da rade radi kan makomar tsohon shugaban na jama’iyyar National People's Congress, NPC, a birnin Chongqing, da ke kudu maso yammacin kasar.Rohotannin da kafafen yada labarum kasar suka bayar, na nuna cewa Bo na da tambayoyin da zai amsa kan kisan wani dan kasuwa, mutumin Britaniya, da matar shi Gu Kailai ta aikata, lamarin da ya yi sanadiyyar zubewar mutunci shi a kasar.