Syria

Sasanta rikicin kasar Siriya ya sami cikas

Rikicin kasar Siriya
Rikicin kasar Siriya

Wani mummunan harin bom, da aka dana cikin mota, ya dawo da hannun agogo baya, a shirin sasanta tsakanin bangarorin da ke rikici da juna a kasar Siriya, sa’oi kadan da fara sasantawar, yayin da ake bukukuwan Sallar layya. Kafafen yada labaru, mallakin gwamnatin kasar sun zargi ‘yan tawayen kasar, da gwamnatin ke kira ‘yan ta’adda, da laifin kitsa harin, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 8, da raunata a kalla 30.Wata kungiyar kare hakkin dan Adam a kasar tace an kai wani mummunan harin na daban, a birnin Daraa, da ke kudancin kasar.