Isa ga babban shafi
Isra'ila-Iran

Isra’ila ta Zargi Iran da Hura Wutar rikicin Gaza

Harin Roka da Hamas ta harba a birnin Ashkelon a Isra'ila
Harin Roka da Hamas ta harba a birnin Ashkelon a Isra'ila REUTERS/Darren Whiteside
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
1 min

Shugaban Yahudawa Shimon Peres ya zargi Iran a matsayin kasar da ke Zuga Falesdinawa domin ci gaba da harba Rokoki a yankunan Isra’ila maimakon shiga tsakani domin kawo karshen rikicin. Shugaban ya jinjina wa Muhammed Morsi na Masar akan rawar da ya ke takawa wajen kawo karshen rikicin.

Talla

“Ba mu jin dadin Iran. Ita ce ke zuga Hamas domin ci gaba da kai hare hare tare da taimaka ma su da makamai”. Inji Peres a lokacin da ya ke zantawa da kafar Telebijin ta CNN.

Shugaba Peres yace ya zama dole Isra’ila ta kaddamar da hare hare akan Hamas a Gaza duk da rayuwar fararen hula da ke salwanta, yana mai cewa sun kai hare hare ta sama kimanin 1,200 tsawon kwanaki Shida.

Shugaban yace Isra’ila ba za ta farwa Iran da yaki ba amma za su yi kokarin dakile hanyoyin da Iran ke bi wajen taimakawa kungiyar Hamas da makamai.

Sai dai kuma shugaban ya bayyana fatar samun tsagaita wuta a Gaza.

Yanzu haka dai Bangarorin Falesdinawa guda biyu, Kungiyar Fatah da Hamas sun amince su hada kai, don fuskantar barazanar Isra’ila da ke ci gaba da kashe Al'ummar su a Gaza.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.