Palasdinu

Bankin duniya zai samar da ruwan sha a Gaza

Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas
Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas

BANKIN Duniya yace zai kashe Dalar Amurka miliyan shida da rabi, wajen samarwa Palasdinawan dake Gaza ruwan sha, da kuma magudanar ruwa, bayan kwanai takwas da Israila ta kwashe tana ruwan wuta a Yankin.Daraktan Bankin mai kula da Gabar Yamma da kogin Jordan da Gaza, Mariam Sherman, tace sun damu da yadda ake fama da matsalar tsabtacacen ruwan sha a Gaza, kuma suna fatar matakin zai taimaka.