Isra'ila-Felesdinu

Isra’ila ba ta da hurumin yin adawa da daga darajar Falasdinawa- Olmert

Tsohon Shugaban Masar'Hosni Moubarak da Tsohon shugaban Falasdinawa Yasser Arafat da tsohon Firaministan Isra'ila Ehud Barak a wani taron sasana rikicin Isra'ila da Falasdinawa da Masar ke shiga tsakani
Tsohon Shugaban Masar'Hosni Moubarak da Tsohon shugaban Falasdinawa Yasser Arafat da tsohon Firaministan Isra'ila Ehud Barak a wani taron sasana rikicin Isra'ila da Falasdinawa da Masar ke shiga tsakani Reuters

Tsohon Firaministan Isra’ila, Ehud Olmert, yace ba su da hurumin kin amincewa da daga darajar kasar Falasdinu a matsayin ‘Yar kallo a zauren Majalisar Dinkin Duniya. Ya kuma ce gina sabbin gidaje a yankunan Falasdinawa bai dace ba.

Talla

Olmert wanda ake saran zai bayyana shirinsa na shiga takarar zabe mai zuwa, yace shirin Isra’ila na gina sabbin gidaje a Yankunan Falasdinawa bai dace ba, yana mai cewa lokaci na kurewa na tattaunawa da Falasdinawa domin samun dawamammen zaman lafiya.

A ranar 29 ga watan Nuwamba ne Falasdinawa suka samu nasarar samun kujerar 'Yan kallo a zauren Majalisar Dinkin duniya bayan kwashe shekaru suna gwagwarmaya duk da adawar Isra'ila da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.