Abbas ya yi kiran samun hadin kan Hamas da Fatah

Shugaban Falasdiniwa Mahmoud Abbas a lokacin da yake jawabin a Zauren Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Falasdiniwa Mahmoud Abbas a lokacin da yake jawabin a Zauren Majalisar Dinkin Duniya REUTERS

Shugaban Falasdinawa, Mahmud Abbas, yace lokaci ya yi da kungiyoyin Fatah da Hamas za su yi watsi da banbance banbancen da ke tsakaninsu, dan tafiya tare. Yayin da yake ganawa da shugabanin Falasdinawa.

Talla

Shugaba Abbas ya ce, lokaci ya yi da zasu dinke barakar su, dan samun wadanda zasu jagoranci cigaba da fafutukar tababtar da kasa ta kansu.

Tun shekara 2006 ake samun rikici a tsakanin bangarorin biyu, lokacin da Hamas ta lashe zaben ‘Yan Majalisun Gaza.

A ranar 29 ga watan Nuwamba ne Falasdinawa suka samu kujerar Yan Kallo a zauren Majalisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.