korea ta Arewa

Kasashen duniya sun yi Allah wadai da harba rokan da Korea ta Arewa ta yi

Kim Jong un na kasar Korea ta Arewa
Kim Jong un na kasar Korea ta Arewa REUTERS/KCNA

Kasashen Duniya na ci gaba da bayyana damuwa tare da yin Allah Waddai da kasar Korea ta Arewa bayan ta harba Tauraronta na Roka a sararin samaniya. Duk da Tankiyar da kasar Korea ta Arewa ke fuskanta daga kasashen Duniya amma kuma ta samu nasarar harba tauraronta a sararin samaniya kwanaki kalilan matashin shugaban kasar ya cika shekara a saman mulki bayan mutuwar mahaishin Kim Jong Il.  

Talla

Kasashen China da Rasha sun bayyana takaicinsu bayan Korea ta Harba Rokan kamar yadda kasar Amurka ta yi Allah Waddai da matakin a matsayin barazana ga tsaro.
Wannan ne kuma yasa kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin duniya ya kira taron gaggauwa akan Korea ta Arwewa.
 

Darajar Kudin Yen dai ta fadi jim kadan bayan Koriya ta bayyana samun nasarar harba Tauraron.

Yanzu haka kuma Duk da barazanar Takunkumi amma gwamnatin Korea ta Arewa ta sha alwashin ci gaba da shirinta tana mai cewa ba zata saurari kwamitin sulhu ba.

Korea ta ce shirinta ba zai zama illa ga kowace kasa ba illa ta yi ne domin girka tauraron dan adam a sama’u.

A watan Afrilu korea ta Arewa ta taba harba Tauraron amma bata samu nasara ba domin rikitowa ya yi a kasa a dai dai lokacin da kasar ke bukin shekaru 100 na haifuwar tsohon shugaban kasar wanda ya mutu Kim Il-Sung bayan mika ya mika mulki ga dansa Kim Jong-un.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.