Pakistan-Afghanistan

Pakistan da Afghanistan sun ce sun fahimci juna a tattaunawar da suke yi

Shugabannin kasashen Turkiya da Afghanistan da Pakistan a lokacin da suke gudanar da taro don sasanta kansu
Shugabannin kasashen Turkiya da Afghanistan da Pakistan a lokacin da suke gudanar da taro don sasanta kansu Reuters

Shugabannin Kasashen Pakistan da Afghanistan sun bayyana samun ci gaba a tattaunawar da suke yi, wadda Turkiya ke shiga tsakanin a Ankara. Taron ya biyo bayan harin wani Dan kunar bakin wake kan shugaban leken asirin Afghanistan, Asadullah Khalid.

Talla

Yayin ganawa da manema labarai, shugaba Hameed Karzai yace an samu fahimtar juna a taron da shugabanin uku da suka hada da Asif Ali Zardari da Abdullahi Gul suka halarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.