Koriya ta Arewa

Mutanen Koriya ta Arewa sun gudanar da Bukin samun nasarar harba Tauraronsu a Samaniya

Daruruwan Al'ummar kasar Koriya ta Arewa ne suka fito suna raye raye domin bukin samun nasarar harba tauraronsu a Samaniya
Daruruwan Al'ummar kasar Koriya ta Arewa ne suka fito suna raye raye domin bukin samun nasarar harba tauraronsu a Samaniya Reuters

Daruruwan Mutanen Koriya ta Arewa ne suka gudanar da bukin murnar samun nasarar harba Tauraron roka a sararin samaniya, duk da adawar da kasashen duniya ke yi da matakin. Gwamnatin kasar tace za ta ci gaba da harba rokokinta a samaniya domin samun ci gaban Kimiya da Fasaha da Tattalin arziki

Talla

Gwamnatin Korea ta Arewa ta samu nasarar harba Tauraron ne kwanaki kalilan al’ummar kasar su gudanar da bukin cika shekara da mutuwar Kim Jong-Il mahaifin shugaban kasar na yanzu Kim Jong-un.

Bayan harba tauraron a samaniya, kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah waddai da matakin, kuma kasashen Yammaci sun ce Koriya ta Arewa ta zama barazana ga kasashen Duniya.

Kasar Amurka tace Matashin Shugaban yana neman ya jefa kasar cikin Rikici.

Kafofin yada labaran Koriya ta Arewa sun ce shugaban mai shekaru 20 yace baya tsoron komi kuma wannan somin tabi ne domin gwamnatin shi za ta ci gaba da harba taurarinta a samaniya.

Matashin Shugaban kasar yace sun harba tauraron ne don samun ci gaban kimiya da Fasaha da tattalin arziki sabanin tunanin kasashen Yammaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.