Pakistan

‘Yan bindiga sun kai jerin hare hare ga ma’aikatan Polio a Pakistan

Wasu da aka jikkata a hare haren da aka kai a Peshawar
Wasu da aka jikkata a hare haren da aka kai a Peshawar REUTERS/Khuram Parvez

‘Yan Bindiga sun bude wuta tare da kai jerin hare hare ga ma’aikatan lafiya da ke aikin riga-kafin cutar shan inna ko Polio a kasar Pakistan. Rahotanni sun ce mutane Shidda suka mutu a wani hari da aka kai a yankin arewa maso gabacin kasar.

Talla

‘Yan sandan Pakistan sun ce suna gudanar da bincike domin gano wadanda ke kai hare haren da kuma dalilin da ya sa suke kai wa jami’an Polio hari.

Kasar Pakistan dai tana cikin kasashe Uku masu fama da cutar Polio, kuma akan haka ne gwamnatin kasar tare da taimakon Majalisar Dinkin Duniya aka kaddamar da rigakafi domin magance cutar.

Sai dai tun da aka fara rigakafin ake samun jerin hare hare daga ‘Yan bindiga inda aka kashe wani jami’in kiyon lafiya a Karachi a ranar Litinin, a jiya Talata kuma wasu mutane uku aka bindige a Peshawar.

Tuni dai kungiyar Taliban ta haramta gudanar da rigakafin cutar Shan-inna a Waziristan tana mai Allah waddai da matakin da aka yi amfani wajen kashe Osama Bin Laden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI