Koriya ta Kudu

Shugabar Korea ta Kudu tace sasantawa da Koriya ta Arewa ne babban kalubalenta

Park Geun-hye sabuwar shugabar kasar Koriya ta Kudu
Park Geun-hye sabuwar shugabar kasar Koriya ta Kudu REUTERS/Kim Jae-Hwan/Pool

Zababbar Shugabar kasar Korea ta Kudu Park Geun-hye, tace barazanar tsaro daga korea Ta Arewa shi ne babban kalubalen da za ta fuskanta bayan ta lashe zaben shugaban kasa. Amma tace za ta nemi komawa teburin sasantawa da mahukuntan Korea ta Arewa.

Talla

Park, ta samu rinjeyen kuri’u ne fiye da abokin takararta Moon Jae-in a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Laraba.

A lokacin da ta ke karrama kabarin mahaifinta tace za ta samar da sabuwar Gwamnati ga mutanen Koriya. Sai dai har yanzu Mutanen Koriya ta Arewa ba su ce komi ba game da nasarar da Perk ta samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.