Isa ga babban shafi
Afghanistan

Wata ‘Yar Sanda ta bindige Wani Jami’in NATO a Afghanistan

Jami'an tsaron kungiyar Tsaro ta NATO a birnin Kabul
Jami'an tsaron kungiyar Tsaro ta NATO a birnin Kabul Reuters/Ahmad Masood
Zubin rubutu: Nasiruddeen Mohammed
Minti 1

A kasar Afghanistan, wata mace ‘Yan sanda, ta harbe wani jami’I farar hula, da ke aiki da kungiyar tsaro ta NATO ko OTAN. Wannan shi ne karon farkon da aka samu mace a kasar Afghanistan da ta kai wa Wani hari a birnin Kabul, kuma tuni aka tsare matar.

Talla

Wannan ne na baya-baya, a jerin hare-haren da ke dakile amincin da ke tsakanin sojojin NATO, da jami’an tsaron kasar ta Afghanistan.

A wani harin na daban kuma, wani jami’in da ke kula da wani ofishin ‘Yan sandan yankin Jawzjan, da ke arewacin kasar, ya bindige abokan aikin shi 5, tare da canza sheka zuwa fadawa kungiyar Taliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.