Iran

An tube ministar kiwon lafiya ta kasar Iran daga kan mukaminta

O presidente iraniano, Mahmoud Ahmadinejad, em Hanói, Vietnã, nesta sexta-feira.
O presidente iraniano, Mahmoud Ahmadinejad, em Hanói, Vietnã, nesta sexta-feira. REUTERS/Kham

Shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmedinajad, ya sallami Ministar Kiwon lafiyar kasar, Marzieh Vahid Dasterjadi, wacce ita ce mace kadai a jerin ministocin kasar.

Talla

Musabbabin korar ministan ta kiwon lafiya, kamar yadda rahotanni suka nuna, ya biyo bayan kiran da Vahid ta yi, na a kara farashin magunguna a kasar ne, saboda tabarbarewar darajar kudin Rial idan aka kwatantata da Dalar Amurka.

Sai dai shugaba Ahmedinajad, bai ji dadin wannan shawara da Vahid ta bayar ba, inda ya yi watsi da ita ya kuma tube ta daga kan mukaminta.

Kasar Iran dai ta kasance kasa, wacce ke hada kashi 97 a cikin kashi 100 na magungunan da take amfani da su a cikin gida, sai dai wasu daga cikin sinadaran da ake hada magungunan, shigo da su ake yi daga kasashen ketare.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.