Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa tace tana shirin sake gwada harba makaminta

Tauraron roka da Koriya ta samu nasarar harbawa a baya
Tauraron roka da Koriya ta samu nasarar harbawa a baya REUTERS/KCNA

Kasar Koriya ta Arewa tace tana shirin gwada makamin Nukiliyanta karo na uku, domin yin kafada da China da Japan da India da suke sahun gaba a duniya ga ciban samar da tauraron Dan Adam.

Talla

Ma’aikatar ilimi da kimiya da Fasaha tace a makon gobe ne aka shirya harba makamin bayan dage lokacin har sau biyu.

A daya bangaren kuma Hukumar tsaron kasar Koriya ta Arewa tace wannan wani martani ne ga jerin takunkumin da Amurka da kawayenta suka kakaba wa kasar.

Wasu masana Kimiya suna tunanin sabon makamin da koriya za ta harba zai iya zama mai aiki da sinadarin uranium, wanda hakan zai nuna yadda kasar ta kware wajen kera makamin Nukiliya.

Koriya ta Arewa ta samu nasarar gwada harba Makamin Nukiliyarta sau biyu, a shekarar 2006 da 2009. Kuma gwajin da kasar ke shirin yi na uku yana zuwa ne bayan Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah Waddai da tauraron da koriya ta harba a kwanakin baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.