Iran

Iran ta tura biri zuwa duniyar wata

Birin da Iran ta tura diniyar wata
Birin da Iran ta tura diniyar wata REUTERS/Press TV via Reuters TV

Iran, ta kafa wani abin tarihi wajen samun nasarar aikewa da biri duniyar wata, al’amarin da ya bata karfin guiwar cewa dan adam na iya tafi kuma ya dawo ba matsala.Ministan Tsaron kasar ta Iran, Janar Ahmad Vahidi ya bada tabbacin samun wannan nasara a tattaunawa da aka yi dashi a gidan Talibijin din kasar kasar, inda yake fadin cewa samun wannan nasara zai bada kafar yin yadda ake so yanzu, kamar ma yadda wasu masanan ke kararwa.A baya, kasar Iran tayi irin wannan kokari ba tare da samun nasara ba, kafin a tsakiyar wannan watan ta furta zata aika da wannan biri sararin samaniya.Gidan Talibijin din kasar, ya yi ta nuna hoton wannan birin, da yadda aka yi dabarun daddaureshi a wata kujera, irin ta jira-jirai, kafin a chusa shi cikin kumbon da yayi jigilar da shi.Matakan chilla birin, zuwa duniyar wata, da Iran tayi, na kara firgita kasashen turai dake ganin samun wannan nasara na iya sa kasar ta chilla wani makamin nukiliya da zai iya dama lissafi.Kafin chilla wannan biri, Iran ta aike dasu bera, har ma da tana, kuma tsarin ta shine nan da shekarar 2020, mai son zuwa duniyar wata zashi.