Iran

An nemi Ahmadinejad da ya kaucewa yin katsalandan a wasu kasashen larabawa

shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmedinejad.
shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmedinejad. REUTERS/Brendan McDermid

Babban Malamin Masallacin Al-Azhar, a brinin Al Kahira Ahmed al-Tayyeb, ya nemi Shugaban Iran Ahmadinejad da ke ziyara a Masar ya kaucewa yin kazalandan ga harakokin kasar Bahrain da sauran kasashen Larabwa tare da kyautata rayuwar mabiya Sunni a kasar shi. Wannan ne dai karon farko cikin shekaru sama da 30 da wani Shugaban Iran ya kai ziyara a kasar Masar.  

Talla

Kuma Ahmadinejad ya samu tarba daga Shugaba Muhammed Morsi.

A wani bangaren kuma, bayan kwashe kwanaki ana kai kawo tsakanin Iran da gungun manyan kasashen Duniya Amurka da China da Rasha da Birtaniya da Faransa da kuma Jamus, kasashen sun tabbatar da cewa zasu gana a kasar Kazakhstan a ranar 26 ga watan Fabrairu domin tattauna kan batun Nukiliyar Iran.
 

Sai dai masana suna hasashen sasantawa da Iran abu ne mai wahala.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.